HomeWorldKasashe 52 na son MDD ta haramta wa Isra'ila sayen makamai...

Kasashe 52 na son MDD ta haramta wa Isra’ila sayen makamai – DW – 11/03/2024

Date:

Related stories

Turkey fires pro-Kurdish mayors, citing ‘terrorism’ – DW – 11/23/2024

Two Turkish opposition mayors were removed from office, Ankara said...

Vigil for Dersim Municipality on its 2nd day

The vigil that started after Dersim co-mayor Cevdet Konak...

Co-Mayor of Hakkari sentenced to 9 years in prison

The final hearing of the lawsuit filed against Hakkari’s...

Cedi-inspired Türkiye triumph over Hungary

ISTANBUL (Turkiye) - Just one win away from FIBA...
spot_imgspot_img

Kasar Turkiyya ta mika wa Majalisar Dinkin Duniya wasikar bukatar haramta wa Isra’ila cinikin makamai, mai dauke da sa hannun kasashe 52 na duniya.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana hakan a kasar Djibouti, lokacin wani taro kan alaka da ke tsakanin Turkiyya da Afirka, yana mai ayyana masu sayar wa Isra’ila makaman a matsayin masu taimaka mata wajen aikata kisan kare dangi.

Karin bayani:Olaf Scholz na Jamus na ziyara a Turkiyya kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Daga cikin kasashen da suka sanya hannun wannan wasika akwai Saudi Arebiya da Brazil da Algeria, sai China da Iran da kuma Rasha.

Sai kuma kungiyar kasashen Larabawa ta Arab League da kuma ta hadin kan musulmi wato Organization of Islamic Cooperation.

Karin bayani:Erdogan ya nemi a kakaba wa Isra’ila takunkumi kan makamai

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba wa Isra’ila takunkumin hana sayen makamai, a matsayin mafita tilo ta kawo karshen yakin Gaza.

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

spot_img