HomeWorldHare-haren Turkiyya a Syria sun jefa mutum miliyan ɗaya cikin ƙangin rashin...

Hare-haren Turkiyya a Syria sun jefa mutum miliyan ɗaya cikin ƙangin rashin ruwa – BBC News Hausa

Date:

Related stories

spot_imgspot_img

Bayanan hoto, Mazauna Hasaka yanzu suna rayuwa ne da ruwan da motocin ɗaukar ruwa ke kawo musu

  • Marubuci, Namak Khoshnaw, Christopher Giles and Saphora Smith
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye

Hare-haren Turkiyya a arewa maso gabashin Syria da ke fama da matsanancin fari ya sake jefa kusan mutane rabin miliyan da ke zaune a yankin cikin rashin wutar lantarki, matakin da masana suka ce ya saɓa dokokin duniya.

Turkiyya ta kai hare-hare sama da 100 a tsakanin watan Oktoban 2019 zuwa Janairun 2024 a cibiyoyin man fetur da na gas da na makamashin ƙasar, kamar yadda wasu alƙaluma da BBC ta tattara suka bayyana.

Hare-haren sun ƙara ta’azzara rayuwar ƙuncin da mutanen yankin suke ciki bayan shekaru da aka ɗauka ana yaƙin basasa a ƙasar da kuma matsanancin fari da sauyin yanayi ya jawo.

Tuni ƙarancin ruwa ya ta’azzara, amma hare-haren a cibiyoyin samar da wutar lantarki a watan Oktoban bara ya ɓarnata asalin tashar ruwan yankin da ke Alouk, wanda hakan ya sa tun lokacin ta daina aiki. A ziyara zuwa tashar sau biyu da BBC ta yi, ta gano cewa mutanen yankin suna fama da ƙarancin ruwa.

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

spot_img